Ba Zamu Lamunci Shaye-Shayen Matasa A Kano Ba – Kwamitin Gwamnati
Kwamitin Yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi da kwacen waya na Gwamnatin Jihar Kano, ya gargadi masu aikata laifuka kan cewar, Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba zata zubawa matasan da ke shaye-shaye da kwacen waya ido ba, a jihar.
Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban Kwamitin, Birgediya Janar mai ritaya, Gambo Mai-Adua, ya yin wani taron manema labarai da kwamitin ya gudanar kan yakin da ya ke da ta’ammali da miyagun kwayoyi, da kwacen waya, a jihar nan. A cewarsa dai, wani rahoto da aka fitar a yan kwanakin nan, ya bayyana yadda a cikin dukkanin mutane shida, mutum guda ya ke ta’ammali da kwayoyi, wanda hakan ya kasance babban kalubale kan yakin da gwamnati ke yi da ta’adar ta shaye-shaye.
Ya kuma bayyana cewar, Kwamitin wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar tun a watan Oktoban 2023, ya na aiki da sauran hukumomin da ke ya ki da shaye-shayen miyagun kwayoyi da laifukan da ke da alaka da shi, wajen tabbatar da kwamitin ya sauke nauyin da aka dora masa, ya na mai karawa da cewar, Kwamitin zai yi aiki da kotun tafi da gidanka, dan ganin an gaggauta hukunta wadanda aka samu da aikata ba dai-dai ba.
Mai-Adua, ya kuma ce Kwamitin ya na kuma fatan ganin wadanda aka samu da aikata shaye-shayen sun gyara halayensu, dan zama masu amfanarwa ga al’umma.