Siyasa

Ba Zan Sake Neman Muƙami Ba, Bayan Kammala Zangon Mulkina – Gwamna AA Sule

Gwamnan jihar Nasarawa, ya bayyana cewar, ba shi da wani shiri na sake neman kujerar siyasa, bayan kammala zangon mulkinsa a matsayin Gwamnan jihar Nasarawa.

Sule, ya bayyana hakan ne, ya yin da ya ke jawabi kan nasarar da ya samu a Kotun Ƙoli, game da ƙarar da Ɗan takarar Gwamna a jam’iyyar PDP na jihar, David Ombugadu , tare da Jam’iyyarsa su ka ɗaukaka a Kotun, su na ƙalubalantar hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara, wanda ya sake tabbatar masa da nasara, a matsayin halastaccen Gwamnan jihar.

AA Sule, ya kuma bayyana wannan matsaya tasa ne, ta cikin shirin ‘Politics Today’ na tashar Talabijin ta Channels, jim kaɗan bayan samun nasarar tasa.

Kotun Ƙolin mai Alƙalai biyar, ƙarƙashin Jagorancin Mai Shari’a, Kudirat Kekere- Ekun, ta ce ɗan takarar na PDP, David Ombugadu, tare da Jam’iyyarsa, ba su da wadattun hujjojin bayyana kansu a matsayin waɗanda su ka lashe zaɓen, ba ya ga rashin hurumin hakan, wanda ke zama uwa uba.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button