Kimiyya Da Fasaha
Babbar Magana : Mutane Na Cigaba Da Zuba Hannayen Jari Akan Fasahar Dawo Da Matattu
Kamfanin Revival Technology Su na Cigaba Da Samun Maƙudan Kuɗaɗe Da Hannun Jarin Miliyoyin Daloli,
Saboda Yunƙurinsu Na Samar Da Wata Fasaha Da Zata Iya Dawo Da Wanda Ya Mutu Duniya.
A yanzu haka akwai sama da mutane dubu shida wadanda suka biya maƙudan kuɗaɗe da zummar duk lokacin da suka mutu a ajiye gawarsu har sai an gama binciken yanda za’a dawo dasu duniya, a inda wasu kuma suka biyawa ƴan uwansu waɗanda su ka jima da mutuwa.
Allah ya kyauta!, Mu dai a Musulunce munsan cewar, babu wanda ya ke da ikon kashewa, ko rayar da wanda ya mutu, sai Allah Subhanahu Wata’ala, wannan kuma bincike da kamfanin Revival Technology ya ke gudanarwa, munsan cewar har abada ba zai taɓa cimma gaci ba.