Labarai

Babu Abin Da Ya Haɗa Najeriya Da Talauci, Zan Samar Da Sauyi Na Din-Din-Din — Tinubu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewar babu abin da ya haɗa Najeriya da talauci, rashin tsaro, da ma rashin cigaba, saboda albarkar Jama’ar da Ubangiji ya azurtata da su.

Inda ya jaddada cewar, ƙarƙashin Jagorancinsa ƙasar za ta cimma tarin nasarori da dama, tare da samun sauyi na din-din-din, domin shi ba Shugaba ne, da zai saurara, ko bayar da uzuri ba.

Shugaban ƙasar ya bayyana hakane ya yin da ya ke karɓar baƙuncin wata tawaga daga jihar Rivers, da ke Kudu Maso Kudancin ƙasar nan, a Fadar Gwamnatin tarayya, da ke Abuja, a ranar Alhamis.

Tawagar mai mutane 62, bisa Jagorancin Gwamna Siminalayi Fubara, ta ƙun shi Shuwagabannin Manyan Jam’iyyun jihar, APC mai mulki, da PDP da ke zama babbar jam’iyyar adawa.

Ka zalika, Tsohon Gwamnan jihar Rivers, Nyeson Wike, tare da Tsohon Shugaban ƙungiyar Lauyoyi ta NBA na ƙasa, Onueze Okocha, su ma sun kasance daga cikin tawagar.

“Ba a yi mu dan mu kasance talakawa ba. Kuma akwai yadda za mu yi mu kai tudun mun tsira. Shi ne ma abin da mu ka sanya a gaba.

“Mu ba malalata bane. Muna kuma da arziƙi dai-dai gwargwado. Kawai muna buƙatar zama ƴan uwa, kuma maƙobta na gari ga junanmu ne.

“Ni ba Shugaba ne da zan saurara ba. Zan yi aiki tuƙuru wajen ciyar da ƙasarmu gaba, ta hanyar nuna ƙwazo, kishi, da ma jajircewa, wajen ganin dukkannin ƴan Najeriya sun yi Arziƙi. Babu dalilin da zai sa mu kasance talakawa! Ba zamu kalli baya ba, za mu tsula da gudu zuwa gaba ne.

“Ta yiwu a yanzu muna ninƙaya ne. Amma da sannu za mu taso sama. Za mu cimma muradan da mu, da waɗanda su ka gabace mu su ke mafarki. Mutanen ƙasa sun zaɓe ni, a yanzu kuma ina jagorantarsu”, a cewarsa.

A nasa jawabin tun da fari, Gwamnan jihar ta Rivers, Fubara, ya bayyanawa shugaban ƙasar cewar, tawagar tasu, wacce ta haɗar da Shuwagabannin jam’iyyun siyasa, da ma Shuwagabannin jihar na yanzu, da na baya, sun ziyarce shi ne, domin miƙa masa saƙon godiya.

Inda ya bayyanawa Shugaban farincikinsu bisa naɗa ɗan asalin jihar, Nyeson Wike, a matsayin Ministansa, ba ya ga tarin muƙamai mabanbanta da ya gwangwaje ƴan jihar da su.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button