Labarai

Babu Batun Sauyawa Hukumomi Matsugunni Zuwa Lagos – Kashim Shettima

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ƙaryata jita-jitar cewa, Gwamnatin tarayya na shirin sauyawa wasu hukumomi matsugunni, zuwa Lagos, daga babban birnin tarayya Abuja.

Shettima, ya bayyana hakan ne, ta bakin mai bashi shawara kan al’amuran siyasa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, a ya yin taron Laccar tunawa da Ahmadu Bello, karo na 10, da ta gudana ranar Asabar, 27 ga watan Janairun da mu ke ciki, a Maiduguri.

“Babu gaskiya, kan jita-jitar da ake yaɗawa na cewar, Gwamnatin tarayya za ta sauyawa wasu daga cikin hukumominta matsugunni zuwa Lagos, daga babban birnin tarayya Abuja, domin kuwa Gwamnatin bata fitita wani ɓangare akan wani”, a cewarsa.

“Na maimaita, Gwamnatin Tinubu ba zata fifita wani sashe akan wani ba, domin kuwa ya na fatan ciyar da ƙasar gaba ne, baki ɗaya “.

Da ya koma kan batun tsaro, wanda shi ne babban maudu’in da aka tattauna a taron, Shettima ya bayyana cewar, ƙasar nan ita ce abu na farko da gwamatin Tinubun ke fatan ciyarwa gaba.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button