Kasuwanci

Babu Ma’aikacin Da Ke Ɗaukar Ƙasa Da Naira 100,000 A Najeriya Da Zai Iya Kai Labari – Majalissar Wakilai

Majalissar wakilai ta ƙasa, ta kafa kwamitin da zai yi aikin zaƙulo mata mafi ƙarancin albashin da ya dace ma’aikatan ƙasar nan su dinga karɓa, dan dacewa da halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki.

Ɗaukar wannan mataki kuma ya zo ne, bayan gabatar ƙudurin haɗin gwuiwar membobin majalissar guda 40.

Da ya ke gabatar da ƙudurin a madadin sauran ƴan majalissa, Aliyu Sani Madaki, ba jam’iyyar NNPP daga jihar Kano, ya ce a halin da ake ciki na hauhawar farashi, abu ne mawuyaci ga mafi yawan ƴan Najeriya su iya mallakar abinci, ruwa, muhalli, Ilimi, kiwon lafiya, zirga-zirga, har ma da sutura.

Ya kuma ce, tashin gwauron zabin farashin kayayyakin da ake cigaba da samu, na shafar tsadar abinci, muhalli, Ilimi, harma da sufuri.

Ɗan Majalissar, ya kuma tunawa ƴan majalissar batun tallafin rage raɗaɗin da gwamnatin tarayya ta ɓullo da shi, bayan cire tallafin mai a watan Mayun 2023.

Ya kuma ƙara da bayyana yadda hakan ya taka gagarumar rawa wajen ƙara ɗaga farashin abinci, da sauran kayayyaki.

Madaki, ya ce ba abu ne mai yiwuwa ba a wannan yanayin da ake ciki, ma’aikaci ya iya rayuwa da albashi ƙasa da Naira 100,000.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button