Babu Soyayya Tsakanina Da Umar M. Shariff – Jaruma Amal Umar
Jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood), Amal Umar, ta bayyana cewar, babu Soyayya a tsakaninta fitaccen Mawaƙi, kuma Jarumi a masana’antar, Umar M. Shariff.
Amal ta ƙaryata zargin soyayyar tasu ne, a ranar Alhamis, ta cikin shirin ‘Daga Bakin Mai Ita’ wanda sashen Hausa na BBC ke gabatarwa, inda ta ce, babu abin da ke tsakaninta da Mawaƙin face zumunci, da kyakykyawar alaƙa.
A gefe guda, Jarumar ta bayyana cewar, ba ta da aminiya a masana’antar, duk kuwa da saninta da aka yi, da fitacciyar Jaruma, Maryam Yahaya, sai dai tace, babu wani abu da ya haɗa ta da jarumar na rashin jituwa, face dai girma, da kuma tarin ayyukan da ya yi wa kowaccensu yawa.
An haifi, Amal Umar ne dai, a birnin Kano, inda ta yi dukkannin rayuwar karatu, ta ke kuma gudanar da sana’arta ta shirin fina-finan Hausa, a jihar.
Ta kuma samu nasarar fitowa a manyan fina-finai irinsu: Ɗan Jarida, Aliya, da makamantansu, ba ya ga tarin bidiyoyin waƙoƙi, da ake tsinkayar fuskar jarumar a cikinsu.