Babu Wanda Ya Kaini Ƙaunar Rarara A Najeriya – Cewar Alhaji Sani
Ɗan Jaridar da ya maka fitaccen Mawaƙin Siyasar nan, Dauda Adamu Kahutu Rarara, a gaban Kotu, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya bayyana cewar, ya na ganin duk Najeriya, babu wanda ya kaishi ƙaunar Rarara, musamman ma a yankin Arewa.
Alhaji Sani, ya bayyana hakan ne, da yammacin ranar Laraba, ta cikin wani saƙo da ya wallafa, a shafinsa na Facebook.
“Nifa a nawa ganin babu wanda ya kaini kaunar rarara a Najeriya musamman a Arewaci.
Gaskiya tanada wuya alaji.”, a cewarsa.
Idan ba a manta ba dai, Alhaji Sani Ahmad Zangina, shi ne mutumin da ya maka Mawaƙin ƙara, a gaban Babbar Kotun Majistiri, mai lamba 1, da ke Lafia, a jihar Nasarawa, bisa zarginsa da furta kalaman tunzura al’umma.
Alhaji Sani Zangina, ya ɗauki matakin gurfanar da Rararan a gaban kotu ne, bayan wasu kalamai da ya furta akan tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, inda ya zarge shi da yin dama-dama a ƙasar nan, kafin miƙata ga Shugaban ƙasa na yanzu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Daga cikin buƙatun da ya gabatar a gaban Kotun kuma, akwai neman kotun ta sanya a tsare Mawaƙin domin bashi kariya, daga barazanar da zai iya fuskanta, daga al’ummar gari.
Kuma tuni aka fara sauraron shari’ar a ranar Litinin ɗin da ta gabata, inda aka ɗage cigaba da sauraron ƙarar zuwa ranar 4 ga watan Disamba, domin bawa Masinjan Kotu damar liƙe takardar sammaci a ɗaukacin gidajen Mawaƙin da ke Najeriya, bayan da ya bijirewa bada damar miƙa masa sammacin hannu da hannu.