Bamu Yi Yarjejeniya Da Tinubu Kafin Samun Nasara A Kotun Ƙoli Ba – Abba Gida-Gida
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa kan cewar, sai da su ka ƙulla yarjejeniya da fadar shugaban ƙasa, kafin samun nasararsa ta Kotun Ƙoli, a ranar 12 ga watan Janairun da mu ke bankwana da shi.
Hakan kuma, na ɗauke ne ta cikin wani jawabi da Babban Daraktan Yaɗa Labarai Da Hulɗa da Jama’a na Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, ranar Litinin, a birnin Kano.
Inda ya ce, babu gaskiya kan wani daftari da ake yaɗawa, wanda ke ɗauke da yarjejeniyoyi huɗu, da aka ce Gwamnatin Kanon ta cimma su da fadar shugaban ƙasa, kafin samun nasara a Kotun Ƙoli.
Ya kuma yi kira ga Jama’a, da su yi watsi da zargin, da ake yaɗawa kan amincewar gwamnan Kanon da batun sauya sheka, daga jam’iyyarsa ta NNPP, zuwa APC mai mulkin ƙasa.
Jawabin, ya kuma ƙara da bayyana cewar, an samar da Majalissar Dattawan Kano ne, domin kawo kawo mafita game da matsalolin da ke addabar jihar, ta fuskar tattalin arziƙi, da siyasa, kuma ra’ayin gwamma, Abba Kabir Yusuf ne kawai, ya sanya ya samar da zauren.
Bugu da ƙari, ya ce Alƙalan sun yi duba da tarin ƙuri’un da talakawa su ka zazzaga Abban ne, wajen yin adalcin tabbatar masa da kujerarsa ba, ba wai saboda akwai wata a ƙasa ba, kamar yadda wasu su ke zargi.
Ya kuma yabawa shugaba Tinubu, kan barin fannin shari’a da ya yi, ya ke cin gashin kansa, tare da tabbatar da adalci, ba tare da tsoma baki cikin al’amuran fannin ba.
Jawabin ya kuma ce, dukkannin ziyarar da Abba Kabir Yusuf ɗin, ya kaiwa Tinubu, a mabanbantan lokuta, basa wuce domin tattauna batun yadda za a ciyar da jihar ta Kano gaba.