Ban Amince Da Auren Alhaji Sani, Saboda Ƙaunarsa Ga Buhari Ba – Hauwa Farouk
Matashiyar nan wacce ta yi shura wajen amfani da shafukan sadarwar zamani, musamman ma ta Facebook, Hauwa Farouk Ibrahim, ta nesanta kanta da labarin da wasu Jaridun Yanar Gizo su ke yaɗawa na cewar, ta aminta da Auren, Alhaji Sani Ahmad Zangina, saboda ƙaunar da ya nunawa tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari.
Hauwa Farouk, ta nesanta kanta da labarin ne, ta wani gajeren saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook, da tsakar ranar Talata, ta na mai bayyana cewar bata da alaƙa da dukkannin wani rubutu da ba a shafinta aka wallafa shi ba.
“Naga wani rubutu yana yawo anata tagging dina a ko ina, banida alaqa da wannan maganar da aka wallafa, duk wani rubutu indai ba wannan account din nawa ya fito ba to ba daga ni bane.. 🙏”, a cewar Hauwa Farouk Ibrahim.
Kafafen Yaɗa Labaran da su ka wallafa Labarin dai, sun zargi Hauwa Farouk da amincewa da Auren Fitaccen Attajirin ne, saboda kyautar danƙareriyar Motar da aka gwangwaje shi da ita, wacce kimarta ta kai Naira miliyan 20, da ma irin ƙaunar da ya ke nunawa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, bayan da ya maka Mawaƙin Siyasar nan, Dauda Adamu Kahutu Rarara, a gaban Kotu, kan wasu kalamai da ya furta, da su ka taɓa muhibbar tsohon shugaban Najeriyar.