Addini

Bana Son Aljannar A Dawo Min Da Kuɗina – Roƙon Wani Kirista Ga Cocin Da Ta Bashi Lasisin Aljanna

Wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuna yadda wani Matashi mabiyin Addinin Kiristanci, ke roƙon Cocin da ta bashi lasisin shiga Aljanna, da ta dawo masa da kuɗinsa.

Matashin, ya miƙa wannan buƙata tasa ga Cocin ne, ta cikin wata ganawa da ya yi da tashar Talabijin ta Arise.

Inda ya ce, ya shiga Cocin ne, a shekarar 2008, ya yin ya zama cikakken memba a shekarar 2011, aka kuma bashi Certificate.

Ka zalika, ya sake yin rijista domin mallakar Certificate na shiga Aljanna kan maƙudan kuɗaɗen da bai bayyana adadinsu ba, hakan kuwa aka yi, inda Cocin ta bashi Certificate na shiga Aljanna jim kaɗan bayan biyan kuɗaɗen.

Sai dai, a yanzu Matashin ya ce, ya biya dukkannin waɗancan kuɗaɗe ne, a lokacin da baya cikin hayyacinsa, dan haka a yanzu ya na buƙatar a dawo masa da kuɗaɗen, domin ya zaɓi ya dawwama a wuta, a madadin yunwa ta kashe shi kafin wa’adinsa ya cika.

Bugu da ƙari Matashin kiristan, ya kuma durƙusar da guiwoyinsa a ƙasa, da nufin bayyanawa hukumar gudanarwar Cocin da ta bashi lasisin cewar, da gaske fa ya ke kuɗinsa ya ke buƙata, ba raha bace.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button