Zamantakewa

Barista Magaji Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Sarkin Gudi, Bisa Rasuwar Ɗan Sa

A ranar Lahadin da ta gabata ne, Jagoran jam’iyyar APC, a jihar Nasarawa, Barista Labaran Shuaibu Magaji, ya kai ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Gudi, bisa rasuwar ɗansa, Alhaji Musa Labaran Sule.

A ya yin ziyarar ta’aziyyar tasa ga Sarkin Mai Daraja ta biyu, a Gudi, da ke ƙaramar hukumar Akwanga, Barista ya bayyana rashin mamacin a matsayin wani babban giɓi da zai wuya a iya cikewa.

Ya kuma roƙi Allah Subhanahu Wata’ala ya jaddada rahama ga ruhin mamacin.

Mamacin wanda ƙani ne ga Gwamna Abdullahi Sule, ya rasu ya bar mata guda da ƴara, kuma tuni aka binne gawarsa, a garin na Gudi, kamar yadda Addinin Musulunci ya yi tanadi.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button