Siyasa

Bayan Hukuncin Kotu : Shugaba Buhari Ya Buƙaci A Bawa Gwamna Ademole Haɗin Kai

A ranar Talatar da ta gabata, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci mazauna jihar Osun da su hada hannu da Gwamna Ademola Adeleke, wajen ganin an gina jihar.

Buharin, ya bayyana cewar, halin da ake ciki a yanzu lokaci ne na nunawa jihar tsantsar kauna, duk da kasancewar ana gabar karshe.

Ta cikin wani jawabi da mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar, ya bayyana hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar Talata, kan zaben gwamnan jihar ta Osun, wacce aka shigar tun ranar 16 ga watan Yulin 2022, a matsayin muhimmiyar gaba a fannin shariá wajen habbaka doka, da ma tsayawar shariá da kafarta, tare da inganta demokradiyya. Inda ya kuma roki daukacin alúmmar kasa, da ma mazauna jihar ta Osun, musammanma haifaffun cikinta da su bawa gwamnatin Sanata Ademola Adeleke hadin kai ta dukkannin fannonin da ta ke bukata, dan ganin ayyuka, da tsare-tsarenta ga dai-daikun mutane da kasuwanci, sun gudana cikin nasara.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button