Zamantakewa

Bayan Shafe Shekaru 12 Su Na Soyayya: Budurwa Da Saurayin Da Su Ka Haɗu A 2go Sun Shirya Shiga Daga Ciki

Wata budurwa da ke gab da zama Amarya, Florence Nwankpa, ta bayyana yadda ta haɗu da sahibinta a kafar sada zumunta ta 2go, tun shekaru 12 da su ka gabata.

Nwankpa, ta bayyana farkon haɗuwar tasu ne, ranar Juma’a, ta shafinta na Instagram, inda ta wallafa tsohon hotonsu, wanda ke nuna tuna baya, tare da kuma hotunan su na gab da Aure (Pre-Wedding Pictures).

Ta kuma rubuta cewar, “Ubangiji shi ne abin godiya 🙏. Dukkannin wata alaƙar soyayya da kuka gani, to tana ɗauke da labarin soyayya😍😍🥰❤️ har gobe 2go shi ne shafin sada zumuntar da nafi ƙauna, domin kuwa ya yi min gagarumar kyautar da ta zarce misaltawa.

“Ina tuna shekarar 2011 lokacin da na haɗu da shi a 2go, ya so ya Aure ni tun a lokacin, amma ban shirya ba. Katsam a wata safiyar Asabar, sai ya halarci Cocin da nake Ibada, ba tare da ya sanar da ni ba.

“Sai ya zauna ta gefena a layin da ke kusa da mu, (Duk da haka ban lura ba, saboda kwata-kwata ban ganshi ba) ya ɗauki hotona lokacin da nake tsaka da Ibada🤣.

“Bayan na koma gida, kwatsam sai na ci karo da hotuna na, waɗanda kuma a kusa da ni aka ɗauke su, a cikin Coci. Na yi fushi, saboda ba a cikin yanayin da ya dace aka yi min hoton ba (Rigar Mahaifiyata ce a jikina, da takalmanta 🤣🤣🤣).

“A haka – a haka, mu ka zama manyan Abokai, amma dai naƙi yarda na haɗu da shi😜. A ranar 6 ga watan Disamban 2013, (ranar bikin birthday ɗina🥰) ya kira domin ya bani kyautar zagayowar ranar haihuwa, na tura ƙanina #belikepresh domin ya karɓo min kyautar.

“Kawai sai na ga ya shigo min hannunsa niƙi-niƙi da zanen hoton Profile Picture ɗina ƙato. Na yi ajiyar zuciya, nace wannan gayen ya latsani.

“Cikin mamaki, na samu gurbin karatu (Admission) a Jami’ar da ta ke jihar da shi ma ya ke karatu😉, a nan ne ma alaƙar da ke tsakaninmu ta ƙara ƙarfi. Bari na gajarce muku labari a yanzu haka….. Aure za mu yi.
#Two2Go2023”.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button