Bayan Shafe Shekaru 70 Bata Samu Rabo ba, Wata Mata Ta Haifi Tagwaye
Rahotanni daga ƙasar Uganda, sun bayyana yadda wata mata da ta shafe tsawon shekaru 70 ba tare da ta yi ko da ɓatan wata ba, mai suna, Safina Namukwaya, ta rabauta da haifar jarirai ƴan biyu.
Wani rahoto da kafar BBC ta wallafa a ranar Alhamis dai, ya tabbatar da cewar, wannan shi ne karon farko da Matar ta taɓa samun ciki a rayuwarta, tsawon waɗannan ɗumbin shekaru.
Namukwaya ta kuma haifi tagwayen ne Mace da Namiji, ranar Laraba, a Asibitin Mata, da ke Kampala, babban birnin ƙasar ta Uganda.
Asibitin ne kuma, ya wallafa labarin haihuwar Matar, ta shafinsa na kafar sada zumunta ta Facebook, ya na mai cewa “Safina Namukwaya, mai shekaru 70 a duniya, ta haifi Yara tagwaye, Mace da Namiji, wannan kuma gagarumar nasara ce, kuma abu ne na tarihi.
“A ya yin da mu ke karrama wannan uwa, tare da yi wa jariranta fatan girma cikin ƙoshin lafiya kuma, kuma muna gayyatarku da ku taya mu farinciki. Wannan labarin ba kawai ya na nuna nasarar da mu ka cimma a aikinmu na Likitanci bane, a’a ya na nuna yadda burin ɗan Adam ya ke iya cika, komai tsawon lokaci”.
Cibiyar IVF, da ke Asibitin ce dai, ta ke ɗaukar ƙoyayen haihuwar Mace, ta kuma haɗa da maniyyin ɗa Namiji, a lura da su, ta hanyar ɗakin Gwaje-Gwaje.