Bayan Shan Dogon Gumurzu, Jami’an Soji Sun Tseratar Da Shanu 2,000
Bayan fafata yaƙi da Jami’an Soji su ka yi, da ƴan bindiga, a ƙaramar hukumar Mariga, da ke jihar Niger, Jami’an sun samu nasarar tseratar da shanu 2,000.
Kafin tseratar da su ɗin dai, wasu ƴan bindiga sama da 500, da su ka fito daga yankin birnin Gwari, a kan babura masu ƙafa biyu fiye da 100 ne, su ka mamaye garuruwa daban-daban, da ke yankin na Mariga.
Kuma shugaban guda daga cikin garuruwan da lamarin ya shafa, Adamu Warari, ya bayyana wa Jaridar PRNigeria cewar, ƴan ta’addar sun je ne da muggan makamai, inda su ka mamaye garuruwa da dama, tare da bankawa wuraren Ibada wuta, da ma ƙona gidaje, da kuma hallaka Magidanta Maza, tare da yin awon gaba da Mata, da ma shanunsu, kafin sanar da Jami’an tsaro.
Da ya ke tabbatar da lamarin, Wani Mai Magana da yawun rundunar Soji, ya bayyana cewar, Jami’an rundunar tasu sun datsi ƴan bindigar tare da Shanun ne, a yankin Bangi, kafin daga bisani su ka sake motsawa zuwa dajin Birnin Gwari.