Bidiyon Dala: Ana Zargin Ganduje Da Yunƙurin Amfani Da Hukumomin Tarayya Wajen Hana Bincikarsa
Ana zargin tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta ƙaddamar bincike kan zarginsa da ake da laifukan rashawa, musamman ma na Faifan Bidiyon Cusa Dala a Aljihu, da fara ɗaukar matakin yin amfani da hukumomin yaƙi da rashawa na tarayya wajen kawo tarnaƙi a binciken da, Muhuyi Magaji Rimingado, ke gudanarwa a kansa.
Idan ba a manta ba dai, Gwamna Gandujen ya samo wani umarnin Kotu, da ya buƙaci hukumar yaƙi da rashawa ta Jihar Kano, da ta dakatar da bincike a kansa, da ma Iyalansa, tare da dukkannin waɗanda ya yi Aiki da su, a muƙaman Siyasa daban-daban, a zangon mulkinsa.
A kwana-kwanan nan dai, an bankaɗo yadda tsohon Gwamna Ganduje da Ƴaƴansa su ka kasance mamallaka wani kamfani, da aka yi amfani da shi wajen karkatar da zunzurutun kuɗi har Naira 4,000,000,000 a zangon mulkinsa, inda kuma hukumar ta kama, tare da tsare su.
Inda kuma, aka sake bankaɗo motocin tarakta masu ɗumbin yawa a gidan ajiye-ajiyensu, da ma zunzurutun kuɗi har Naira 700,000,000 a Asusun Bankin Union, Taj, da ma Zenith Bank da ake zargin an yi hada-hadarsu ta haramtacciyar hanya.
Bugu da ƙari, Jaridar Solacebase ta rawaito yadda a kwana-kwanan ma aka bankaɗo sama da Fulotai 543 da tashar tsandaurin Zawachiki, da aka ƙiyasta kimarsu da Naira 5,000,000,000 da su ma ake zargin Gwamnan ya karkatar da su ta ɓarauniyar hanya, bayan da ya yi amfani da kamfanin Lamash Properties Limited, wanda mallakinsa da Ƴaƴansa ne.
Kuma ana zargin wancan kamfani da mallake wasu kadarorin mallakin Jihar Kano kamar, Daula Hotel da Triumph Publishing Company, ta hanyar wasu raunanan yarjeniyoyi.
Bugu da ƙari kuma, ana zargin Gwamnatin Gandujen da karkatar da sama da Biliyan 100 na kuɗaɗen ƙananan hukumomi.
Wata takarda da aka fitar kuma, ta zargi tsohon Gwamnan da yunƙurin yin amfani da kujerarsa ta Shugabancin Jam’iyyar APC a matakin ƙasa, wajen amfani da hukumomin tarayya, irinsu EFCC da CCB, dan daƙile hukumar rashawar ta Kano, daga bincikenta, ta hanyar buƙatar wasu bayanai da ke kamanceceniya da bincikar Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimingado.
Da aka tuntuɓi Shugaban hukumar ta PCACC Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, domin jin ta bakinsa kan wannan batu kuwa, wayarsa ta kasance a kashe.
Sai dai, Kwamishinan Shari’a na Kano, kuma Atoni Janar, Barista Haruna Dederi, ya ce basu samu wannan buƙata ta EFCC ba zuwa yanzu, sai dai ya ce EFCC da CCB din ba za su iya dakatar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawar ta Kano, daga aiwatar da Aikin da doka ta bata dama ba.