Tsaigumi

Bidiyon Gwale-Gwalen Da Malamin Jami’a Ya Bawa Ɗalibai A Kano, Na Cigaba Da Tada Ƙura

Wani faifan bidiyo, da ke nuna yadda Malami a Jami’ar Kimiyya Da Fasaha ta Aliko Dangote, da ke garin Wudil, a jihar Kano, ke bawa dalibansa Gwale-Gwale ta hanyar sanya su tsallen kwaɗo, tare da haɗa musu da duka, na cigaba da tada ƙura, a kafafen sada zumunta.

Bidiyon wanda ya karaɗe dukkannin lunguna da saƙunan kafafen sada zumunta dai, na bayyana yadda Malamin, wanda ke koyar da darasin GST2201, ke dukan ɗaliban na aji biyu (Level 200), tare da sanya su tsallen kwaɗo ne, bayan da ya zarge su da laifin makara, tare da yin surutu, a ya yin da ya ke koyar da darasin na Nigerian People and Culture.

Daga cikin waɗanda su ka yi martani game da lamarin kuma, har da fitaccen Lauyan nan, Barista Abba Hikima, wanda ya bayyana nasa martanin ta shafinsa na kafar sada zumunta ta Facebook.

Hikima yace, abin da Malamin ya aikata, ya saɓa da sashe na S34 na haƙƙoƙin ƴan ƙasa, da kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya tanadar.

Ya kum yi kira ga Jami’ar, da ta gaggauta ɗaukar mataki akan Malamin, bisa tauye wannan haƙƙi na Ɗalibansa da ya yi.

Har ya zuwa yanzu kuma, hukumar gudanarwar Jami’ar bata ce komai game da lamarin ba.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button