Kasuwanci

BUA Zai Zabge Farashin Buhun Simintinsa Zuwa 3,500

Kamfanin simintin BUA na shirin zabge farashin simintinsa da kaso 40 cikin 100 a ƙasar nan, inda zai ragu daga Naira 5,500 zuwa 3,000 da 3,500.

Shugaban kamfanin na BUA Cement, Abdul-Samad Isyaka Rabi’u, shi ne ya bayyana hakan ga Manema Labarai, jim kaɗan bayan kammala tattaunawarsa da Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a Fadar Gwamnatin tarayya, da ke Abuja.

Inda Abdul-Samad ɗin ya ce, zabge farashin simintin wani sashe ne na gudunmawar da kamfanin zai bayar, wajen ƙarfafa yunƙurin Gwamnatin tarayya na dai-daita farashin kayayyakin amfani.

Sai dai, hakan zai biyo bayan buɗe sababbin kamfanoni biyu, da za su dinga samar da tan miliyan 3 na simintin, da ake sa ran ƙaddamarwa a ƙarshen shekara.

Ya na mai cewa, “Bari na fara da godewa Maigirma Shugaban ƙasa, bisa tarbar da na samu daga gare shi a yau, na zo ne domin na bayyanawa Shugaban halin da kasuwancin simintin da mu ke samarwa ya ke ciki.

“Muna da sababbin kamfanoni biyu na siminti da abin da kowanne zai samar ya kai tan miliyan 3, za kuma mu ƙaddamar da su a ƙarshen shekara.

“Na yi masa bayanin cewar, muna son mu ƙarfafi shirin Gwamnati na rage farashin siminti, da zarar an ƙaddamar da waɗannan jerin siminti biyu, za mu dinga samar da sama da tan miliyan 17 a kowacce shekara, sannan za mu rage farashin simintinmu daga farashin 5,000 ko 5,500 da ya ke a yanzu akan kowanne buhu, zuwa Naira 3,000 da 3,500”.

A cewar sa kuma, kamfanin zai iya aiwatar da hakan ne kawai, saboda a cikin gida (Najeriya) ya ke samar da simintinsa.

“Kaso tamanin na kayayyakin da mu ke amfani da su wajen samar da siminti a Najeriya, daga Limestone da Gypsum su ke, sai dai mu kan buƙaci zafi. Duk da cewar, tabbas mu na da iskar Gas a Najeriya.

“Muna son mu ƙarfafi Gwamnati, muna son goyawa shirinta baya na rage farashin kayayyaki”, a cewarsa.

Inda ya ce, sababbin wuraren sarrafa siminti guda biyu, da Shugaba Tinubu zai ƙaddamar a ƙarshen shekarar nan ta 2023, za su ƙara Adadin simintin da kamfanin ya ke iya samarwa, zuwa metric tan miliyan 17.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button