Buhari Ya Buɗe Gidan Gyaran Hali, A Kano
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ƙaddamar da sabon gidan gyaran hali na zamani, mai ɗaukar kimanin mutane 3,000 a Janguza, da ke jihar Kano.
A ya yin da ya ke jawabi, ta allon gani ga ka, Shugaban ya ce Gwamnatinsa ta fara Aikin gina gidajen gyaran halin na zamani a shiyyoyin ƙasar nan guda shida ne, domin magance matsalar cunkuson da ake fuskanta a wasu daga cikin gidajen da ake da su, wanda hakan ke sanyawa ana shiga cikin haƙƙin ɗaurarru.
A nasa jawabin, Kakakin hukumar kula da gidajen gyaran hali ta ƙasa (NCoS), Abubakar Umar, cewa ya yi sababbin cibiyoyin da gwamnatin Buharin ta samar, za su taka muhimmiyar rawa wajen rage yawan kuɗaɗen da Gwamnati ke kashewa wajen zirga-zirgar masu laifi, daga gidajen gyaran hali, zuwa kotuna, duba da yadda sababbin gidajen gyaran halin na zamani su ke ɗauke da ɗakunan kotuna kimanin guda biyar.
A nasa ɓangaren, Ministan cikin gida, Ra’uf Aregbesola, kira ya yi ga gwamnatocin Jihohi, da su ɗora da aikin ciyar da masu laifin da ake tsare da su.
Da ya ke jawabi, a madadin Gwamnan jihar Kano, Sakataren Gwamnatin jiha, Alhaji Usman Alhaji, bayyana farincikinsa ya yi kan samar da cibiyar, ya na mai cewar zata taimaka matuƙa wajen haɓɓaka ayyukan gidajen gyaran hali.