Siyasa

Buhari Ya Cika Alƙawuransa – Fadar Shugaban Ƙasa

A jiya (Laraba), Fadar shugaban ƙasa ta yi ikirarin cewar, kyakykyawan yanayin Najeriya ya dawo, a ƙarƙashin zangon mulkin shugaba Buhari.

Ta cikin wani jawabi da Maitaimakawa Shugaban ƙasar kan al’amuran yaɗa labarai, Garba Shehu ya fitar, ya ce a wannan gaɓa da ake ciki ta bayan kammala zaɓuɓɓuka gwamnatin tasu ta mayar da hankali wajen ganin bata samu tasgaro kafin barinta karagar mulki ba.

Ya na mai cewar, Shugaba Buhari, ya gaji tattalin arziƙin ƙasar cikin mummunan yanayi, ya yin da rashawa ta yi wa kowanne ɓangare na al’umma da hukumomi katutu, ba ya ga farashin man fetur da ke cikin wani hali, da ma ɗumbin ayyukan ta’addanci da ake gudanarwa, ba ya ga munanan ayyukan Boko Haram, da ma ƴan ta’addan da su ka addabi iyakar ƙasar nan.

Amma da zuwan Buhari, ya nemi taimakon sauran ƙasashen duniya, wanda har ya kaita matakin da ta ke a yanzu.

”A yanzu babu cin hanci da rashawa, saboda tsare-tsaren Gwamnatin Buhari, ba ya ga tallafawa al’ummar ƙasa da aka yi da jari, domin bunƙasa sana’o’insu, wanda ya laƙume miliyoyin daloli, da ma dawo da kuɗaɗen da ƴan siyasa su ka sata, su ka jibge a bankunan ƙasashen ƙetare.

”A yanzu ƴan bindiga basu da mallakin ko gari guda a Najeriya, kuma tuni ma Jami’an tsaronmu su ka kawo ƙarshen shuwagabanninsu”, a cewar sa.

Shehu, ya kuma ce, shi ma tattalin arziƙin ƙasar nan ya farfaɗo, a ƙarƙashin wannan gwamnati.

Ya na mai cewar, ”Asusan ajiyarmu na ƙasashen waje su na cigaba da haɓɓaka, a tsawon waɗannan shekaru takwas”.

Mai magana da yawun Buharin, ya ƙara da bayyana irin rawar da Gwamnatinsa ta taka, a fagen inganta rayuwar ƴan Najeriya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button