Buhari Zai Bar Najeriya Fiye Da Yadda Ya Sameta – Fashola
Ministan Ayyuka da gidaje mai barin gado, Babatunde Fashola, ya bayyana cewar, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, zai bar karagar mulki, a ya yin da Najeriya ta samu cigaban da ya zarce yadda ya sameta, a shekarar 2015.
Fashola, ya bayyana hakan ne, a ya yin zantawarsa da tashar Talabijin ta Channels, cikin shirin siyasa na Politics Today.
A cewar Ministan dai, Gwamnatin Buharin ta cika dukkannin alƙawuran da ta yi wa Talakawa, na kawo sauyi.
Da ya ke bayyana ire-iren cigaban da Gwamnatin ta kawo, ya ce inganta titunan ƙasar nan da ta yi ya sauƙaƙawa jama’a, ta hanyar rage tsawon lokacin da su ke shafewa, a ya yin tafiya, da sama da kaso 55.
Da ya juya kan batun yaƙi da cin hanci da rashawa kuwa, Ministan ya bayyana yadda Gwamnatin Buhari ta samu nasarar dawo da maƙudan kuɗaɗe da dama da aka yi sama da faɗi da su, a Gwamnatocin baya, ya na mai sanar da yadda hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa su ka dinga kamawa, tare da gurfanar da waɗanda ake zargi, a gaban kuliya.