BUK Ta Karrama Barau Jibrin Da Digirin Girmamawa
Jami’ar Bayero, da ke birnin Kano, ta karrama Mataimakin Shugaban Majalissar Dattijai, Sanata Barau I. Jibrin (Maliya), tare da Shugaban kamfanin cigaban Afirka (AfDB), Dr Akinwunmi Adesina, da digirin girmamawa, ya yin bikin ya ye ɗalibanta karo na 38, da ta gudanar.
An karrama Sanata Barau ne dai, da Digirin sanin dokoki wato Doctor Of Laws (honoris causa), ya yin da shi kuma Adesina ya rabauta da Digirin gudanarwar kasuwanci (Doctor Of Business Administration).
Hakan kuma ya zo ne, sakamakon yabawar da Jami’ar ta yi da irin gudunmawar da su ke bayarwa a ɓangaren Ilimi da cigaban matasa, tare da sauran ɓangarori.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya ce an samu amincewar Majalissar Zartarwar Jami’ar, tare da sashen gudanarwarta, kafin miƙa Digirin girmamawar.
Kimanin Ɗalibai 180 daga cikin waɗanda Jami’ar ta yaye ne su ka kammala karatunsu da Digirin Ajin Farko (First Class), ya yin da kimanin 11,284 su ka kammala Digirin farko, sai 317 da su ka kammala PhD, ya yin da 3,770 su ka kammala Digiri na biyu (Masters).