Cancantar Olympic: Ƴan Damben Zamanin Najeriya Takwas Sun Samu Nasarar Zuwa Wasan Daf Da Na Kusa Da Na Ƙarshe
Ƴan damben zamanin Najeriya guda takwas, sun samu nasarar zuwa wasan daf da na kusa da na ƙarshe, a wasan damben zamani , na neman cancantar fafatawa a wasannin Olympic, da ke gudana a babban birnin Dakar, na ƙasar Senegal, inda su ke cike da muradin ganin sun samu nasarar halartar gasar ta Olympic, wacce za ta gudana a kasar Paris, a shekarar 2024.
Ƴan wasan damben zamani tara ne dai, su ka halarci birnin na Dakar, da zummar wakiltar Najeriya, a wasannin na neman cancanta, kuma ɗan wasa Fatai Moshood mai nauyin kg 71 ne kaɗai ya gaza, inda ya sha kaye a ya yin karawarsu da ɗan damben ƙasar Congo, Steve Kulenguluka, a turmi na 32, da su ka fafata a ranar 10 ga watan Satumbar da mu ke ciki.
A ranar Litinin, wacce ke a matsayin rana ta uku, ta gudanar da wasannin damben dai, ƴan wasan Najeriya guda uku, sun nuna bajinta, inda dukkanninsu su ka samu tikitin tsallakawa wasan daf da na kusa da na ƙarshe.
Ɗan wasan Najeriya mazaunin Burtaniya, da ke da gagarumin nauyin jiki, Olaore Adams, ya fuskanci Zahouli Bi Marshal na Ivory Coast, a ɓangaren maza masu nauyin kg 92, kuma aka gaza samun wanda ya samu nasara a zagayen farko.
A wasan ƙarshe da aka gudanar a ranar kuma, Omole Dolapo ne ya doke ɗan wasan ƙasar Ghana, Omar Abdul a ɓangaren maza masu nauyin kg 57, inda ya samu nasara bayan fafata turmi uku.