Kasuwanci

CBN Ya Soke Lasisin Ƙananun Bankuna 179

Babban bankin ƙasa CBN, ya soke lasisin ƙananan bankunan kasuwanci kimanin 179, a faɗin ƙasar nan, ya yin da a gefe guda ya soke lisisin wasu bankuna huɗu, da ma kamfanonin hada-hadar kuɗaɗe guda uku.

Bayanin hakan kuma, na ɗauke ne ta cikin wata sanarwa ta musamman, da Gwamnatin tarayyar ta fitar, wacce aka wallafa ranar Talata, a shafin babban bankin ƙasa (CBN).

Gwamnan bankin na CBN, Godwin Emefiele ne dai ya jagoranci Aikin soke lasisin bankunan, bisa dogaro da sashe na 12, na dokar BOFIA ta shekarar 2020, wacce ta bawa babban bankin ƴancin yin haka.

Soke lasisin bankunan kuma, na nufin an haramta musu cigaba da gudanar da ayyuka a ƙasar nan, har Illa-Masha’Allahu, ko kuma bayan sun cika sharuɗɗan da su ka jawo soke lasisin nasu.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button