Tsaigumi

Cikakken Batu: Dalilai, Zarge-Zarge, Da Buƙatun Da Alhaji Sani Ya Miƙa Wa Kotu, Kan Shari’arsa Da Rarara

Wata takardar shigar da ƙara, mai ɗauke shafuka biyu, da Alhaji Sani Ahmad Zangina, wanda ke ƙarar Mawaƙi, Dauda Adamu Kahutu (Rarara), a gaban Babbar Kotun Majistiri mai lamba 1, da ke, Lafia, a jihar Nasarawa, ya aikowa Jaridar Rariya Online, da yammacin ranar Asabar, ta sake warware cikakken batu kan dalilai, buƙatu, da ma jerin laifukan da fitaccen Ɗan Jaridar ya ke zargin Mawaƙin Siyasa, Rarara, da aikatawa, wanda ya sanya har ya maka shi ƙara a gaban kotu.

Takardar ƙarar mai lamba: CMC1LF/73CA/2023, na ɗauke da kwanan watan 1 ga watan Nuwamban da mu ke ciki. Ga kuma jerin ababen da ta ƙunsa:

•BUƘATA:

Mai ƙara (Alhaji Sani Ahmad Zangina), ya buƙaci Kotun da ta gaggauta bayar da umarnin tsare wanda ake ƙara (Dauda Adamu Kahutu), bisa ƙorafe-ƙorafe kamar haka:

BAYANIN ƘORAFI:

•Mai ƙara Ɗan Jarida ne (Mamallakin Jaridar Rariya Online), mazaunin jihar Nasarawa, wanda a nan Kotun da za ta saurari ƙorafin take.

•Wanda ake ƙara Mawaƙin Siyasa ne, wanda ke zama a Kano da Abuja, wanda ba a nan Kotun da ake ƙararsa ta ke zaune ba.

•A ranar 27 ga watan Oktoban 2023, wanda ake ƙara ya gudanar da taron Manema Labarai a Najeriya, inda ya furta kalaman cin mutunci da tunzura al’ummar ƙasar, kuma wanda ya ke ƙara (Sani Ahmad Zangina) ya na daga cikin Jama’ar da ransu ya ɓaci, saboda kalaman.

•Kalaman cin zarafi, da tunzurin da ya furta sun karaɗe ko ina a Najeriya.

1• Abinda wanda ake ƙara ya aikata na furta kalaman da ke kamanceceniya da yunƙurin tada zaune tsaye, ko tada hankalin jama’a, laifi ne da ke a matsayin barazana ga zaman lafiya, wanda ya saɓa da sashe na 114, na kundin dokokin penal code – Cap 89.

2• Kiran sunaye da wanda ake ƙarar ya yi, a cikin jawabinsa laifi ne na ƁATA SUNA, wanda sashe na 392 na kundin Dokokin Penal Code – CAP 89 ya yi tanadin hukuncinsa.

3• Kiran ɓoyayyen suna/sunan cin mutunci/sunan rashin kimanta wanda ake ƙara akansa, da wanda ake ƙarar ya yi, YUNƘURIN YI WA WANDA YA KIRA TABO NE TA HANYAR ƘARYA, wanda sashe na 393 (1) na kundin Dokokin Penal Code – CAP 89 ya yi tanadin hukuncinsa.

4• Abinda wanda ake zargin, da kalaman da ya furta su ka jawo, bayan isa kunnuwan jama’a, laifi ne na yin AMFANI DA HARSHE MAI CUTARWA, wanda sashe na 399 na kundin dokokin penal code – CAP 89 ya tanadi hukunci akan hakan.

Kotun Majistirin dai, ta sanya ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamban da mu ke ciki, a matsayin ranar da za ta fara sauraron shari’ar.

©RARIYA_ONLINE.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button