Ilimi

Cire Kaso 40 A Harajin Jami’o’i Dai-Dai Ya Ke Da Yunƙurin Kaiwa Jami’o’in Hari – ASUU

Ƙungiyar Malaman Jamióí ta ƙasa, ASUU, tare da Kwamitin Shuwagabannin Jamióín ƙasar nan, , sun bayyana shirin Gwamnatin tarayya na fara cire kaso 40 na kuɗaɗen harajin cikin gida da Jamióín ƙasar nan ke samarwa, a matsayin kaiwa Jamióín hari.

Idan ba a manta ba dai, ta cikin wata wasiƙa da Gwamnatin tarayyar ta aike, tun a ranar 17 ga watan Oktoban shekarar da mu ke ciki, mai taken ‘Ƙaddamar da fara cire kaso 40 kaitsaye daga harajin cikin gida, na Manyan Makarantun Gwamnatin tarayya’, Gwamnatin ta bayyana cewar, za ta fara zaftare kuɗaɗen harajin ne daga watan Nuwamban da mu ke ciki.

Wasiƙar mai ɗauke da sa hannun Akanta Janar ta Gwamnatin tarayya, Mrs Oluwatoyin Madein, Daraktan haraji da sanya hannun jari, na Ofishin Akanta Janar ɗin, Felix Ore-Ofe Ogundairo, ya bayyana cewar, tsarin fara cire kuɗaɗen kaitsaye daga harajin cikin gida na IGR, ya zo ne dai-dai da tsarin gudanar da alámuran kuɗi, da aka fitar, tun a ranar 20 ga watan Disamban 2021.

Sai dai, da ya ke martani kan lamarin, Shugaban ƙungiyar Malaman Jamióí ta ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodoke, ya bayyana cewar, matakin na gwamnatin tarayya abu ne mai taɓa zuciya, ya na mai cewar Jamióí ba sa iya samar da wasu kuɗaɗen shiga daga ayyukan da su ke gudanarwa ga Ɗalibai.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button