Ilimi
College Of Nursing Kano Za Ta Fara Sayar Da Form
Kwalejin Kimiyyar Lafiya Ta Jihar Kano (Kano State College Of Nursing), za ta fara sayar da Form ga ɗaliban da ke sha’awar shiga Kwalejin, a ranar 4 ga watan Maris mai kamawa, ya yin da za a rufe a ranar 8 ga watan goben na Maris.
Farashin Form ɗin Naira 5,000 ne ga ɗaliban da ke son karanta fannin Basic Midwifery, sai kuma Naira 2,000 ga waɗanda ke sha’awar karatun Community Midwifery.
Wajibi ne kuma, waɗanda ke sha’awar karatu a Kwalejin su mallaki aƙalla Credits 5 da ya haɗarda da Turanci, Lissafi, Biology, Chemistry, da Physics a sakamakonsu na kammala Sakandire.
Dukkannin waɗanda ke son cike Community Midwifery kuma, dole ne su kasance ba ƴan ƙaramar hukumar birnin Kano ba (Ƴan Ungogo da Kumbotso za su iya cikewa).