Labarai

CONUA Ta Buƙaci Gwamnati Ta Biya Membobinta Ragowar Albashin Yajin Aiki

Sashen ƴan aware na ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (CONUA), ta buƙaci Gwamnatin tarayya da ta gaggauta biyan membobinta ragowar kuɗaɗen albashinsu na watanni uku da rabi, wanda tace ya rage a hannun gwamnatin, duk kuwa da tsada da tashin farashin kayayyakin da ake fama da shi.

Ya yin da ya ke yabawa ƙoƙarin gwamnatin na biyansu albashin watanni huɗu, daga cikin watanni bakwai da rabi da ASUU ta shafe tana Yajin Aiki, ta cikin wani jawabin Manema Labarai da ƙungiyar ta fitar, a ranar Alhamis, shugaban CONUA na ƙasa, Niyi Sunmonu, ya roƙi gwamnatin da ta biya su ragowar albashin da su ke binta, su na masu jaddada cewar basu shiga cikin Yajin Aikin ba.

Idan za a iya tunawa dai, ƙungiyar ta CONUA ta samu sahalewar zama cikakkiyar ƙungiyar Malaman Jami’o’i ne, tun a wa’adi na biyu na gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button