Da Ɗumi-Ɗumi: Alhaji Sani Ya Maka Rarara A Gaban Kotu
Biyo bayan kaɗa ƙuri’ar neman jin ra’ayin jama’a, kan shirin fitaccen Ɗan Kasuwar nan, Alhaji Sani Ahmad Zangina, na maka Mawaƙi, Dauda Adamu Kahutu Rarara a gaban kotu, a ƙarshe fitaccen Attajirin ya amince da ƙuri’a mafi rinjaye da al’umma su ka kaɗa wacce ke goyon bayan gurfanar da Mawaƙi Rarara a gaban Kotu, domin girbar abin da ya shuka, kuma tuni ya shigar da ƙarar.
Ya yin da Kotu ta sanya ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamban da mu ke ciki, a matsayin ranar da za ta fara sauraron shari’ar da aka gurfanar da Mawaƙin.
Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya gurfanar da Rarara a Kotu ne, bisa zarginsa da furta kalaman da ka iya tunzura jama’a, su ɗauki doka a hannayensu, bayan cin zarafin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta hanyar kushe abubuwan cigaban da Gwamnatinsa ta gudanar, tare da zarginta da damalmala al’amuran ƙasar, kafin miƙata ga sabon shugaba, Bola Ahmed Tinubu.
Daga cikin buƙatun da Fitaccen Ɗan Siyasar ya nema gaban Kotun, akwai ɗaure Mawaƙin na aƙalla tsawon shekaru 10 ko abin da ya yi kama da haka, domin bashi kariya daga abin da ka iya zuwa ya dawo a tsakaninsa da Talakawan ƙasa, da ma cin tarar Mawaƙin wasu maƙudan kuɗaɗe, dukka dai da nufin haska masa kuskurensa.
Abin jira a gani, bai wuce yadda zaman shari’ar zai fara kasancewa tsakanin Fitaccen Ɗan Kasuwar da Mawaƙin mai zamani a fagen Siyasa ba.
Shin ma Rararan zai amsa kiran Kotu na halartar shari’ar, ko kuwa zai sanya ƙafa ya yi fatali da sammacin da aka aike masa ?.
LOKACI SHI NE ZAI BAYYANA ABIN DA KA IYA FARUWA.