Addini
Da Ɗumi-Ɗumi: An Ga Watan Azumi A Saudiyya
Wani saƙo da Fadar Sarkin Saudi Arabia, ta wallafa a shafinta na kafar sada zumunta ta X, a ranar Lahadi, ta bayyana yadda aka yi nasarar tozali da jinjirin watan Azumin Ramadan, a ƙasar.
Hakan kuma na nufin gobe (Litinin), ita ce za ta kasance ɗaya ga watan An Ramadan, a ƙasar.
Ko a nan Najeriya ma, tuni Fadar Sakin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar Na III, ta buƙaci al’ummar ƙasar da su fara duban jaririn watan na Ramadana daga yau (Lahadi), 29 ga watan Sha’aban.