Ilimi

Da Ɗumi-Ɗumi: ASUU Na Barazanar Tsunduma Yajin Aiki

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU), ta bayyana aniyarta ta tsunduma Yajin Aiki, a faɗin ƙasar nan baki ɗaya.

ASUU, ta bayyana hakan ne, a yayin da take tsaka da gudanar da taron manema labarai, yau (Talata), a Jami’ar Abuja.

ASUU ɗin dai, ta zargi Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da nuna halin ko in kula ga fannin Ilimin Jami’o’in tarayya, tare da gaza sabunta Kwamitin gudanarwar Jami’o’i, tun bayan rushe shi da Gwamnatin tarayyar ta yi, tun a shekarar da ta gabata.

Ka zalika, ta ga baiken ƙarin kaso 35 na albashi ga Farfesoshi, tare da kaso 25 ga sauran Malaman Jami’o’i.

Idan ba a manta ba dai, Gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta rushe Kwamitin gudanarwar Jami’o’in ƙasar nan (Governing Council), tun a shekarar 2023, Jim kaɗan bayan karɓar rantsuwarta ta kama aiki.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button