Labarai

Da Ɗumi-Ɗumi: Daurawa Zai Koma Kujerar Shugabancin HISBAH

Hukumar HISBAH ta jihar Kano, ta bayyana cewar, tuni aka samu sulhu, tare da take wuyan shaiɗan kan dambarwar da ta kunno kai a hukumar, wacce ta sanya har shugabanta, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana ajiye muƙaminsa.

Hukumar ta kuma ce, Babban Kwamandan nata zai ci gaba da aiki nan da wani ɗan lokaci.

HISBAH ta yi wannan albishir ga al’umma ne, a ranar Asabar, ya yin zantawarta da gidan Rediyon Freedom, da ke unguwar Sharada, a birnin Kano.

Daurawa, ya bayyana sauka daga muƙaminsa ne dai, a safiyar Asabar, bayan wasu kalamai da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya furta akan hukumar, waɗanda ya ce sun karya masa guiwa kan ƙoƙarin da ya ke yi na inganta ayyukan hukumar, da ma tsaftace jihar Kano, daga dukkannin nau’o’in ayyukan baɗala.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button