Ilimi

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Kano Ta Rage Kuɗaɗen Makaranta, A Manyan Makarantun Jihar Da Kaso 50

Bayanin hakan ya fito ne, ta cikin wani saƙo da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya wallafa a shafinsa na Facebook, cikin daren Litinin, 28 ga watan Augusta.

Inda ya ce, ya buƙaci hakan ne, sakamakon halin matsin tattalin arziƙin da Al’umma su ka tsinci kansu.

Gwamnan, ya kuma ce, sun amince da ɗaukar wannan mataki ne, a ya yin tattaunawarsa da Shuwagabannin Manyan Makarantun Jihar.

“A wannan rana na samu ganawa da dukkanin shugabannin manyan makarantu na gaba da sakandare mallakin jihar Kano inda na basu umarnin su rage kuɗaɗen da ɗalibai ke biya na makaranta kaso hamsin (50%) cikin ɗari sakamakon yanayin matsi da al’umma suke ciki.-AKY”.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button