Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu Ta Bayyana Nasiru Gawuna A Matsayin Halastaccen Gwamnan Jihar Kano
Kotun sauraron ƙarar zaɓen Gwamnan jihar Kano, Mai Alƙalai uku ƙarƙashin Jagorancin Mai Shari’a, Oluyemi-Akintan-Osadebay, ta soke nasarar da, Abba Kabir Yusuf ya samu, a zaɓen Gwamnan Kano, inda ta miƙata ga ɗan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna.
Kotun ta kuma buƙaci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), da ta soke nasarar ta Abba Kabir Yusuf, na NNPP, tare da bawa, Nasiru Gawuna shaidar lashe zaɓe.
Wannan hukunci dai, ya biyo bayan soke ƙuri’u kimanin 165,663 da Kotun ta yi.
Tun da farko, jam’iyyar APC ce dai, ta shigar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, jam’iyyar NNPP, da Abba Kabir Yusuf ƙara a gaban Kotun sauraron ƙarar zaɓen Gwamna, ta na ƙalubalantar nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ku saurare mu, muna tafe da ƙarin bayani.