Siyasa

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu Ta Ci Tarar Tsohon Ɗan Majalissa, Bayan Watsi Da Ƙararsa, A Kano

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan Majalissu, da ke Kano, ta kori ƙarar da tsohon ɗan majalissar wakilai, mai wakiltar ƙananan hukumomin Wudil da Garko, Muhammad Ali Wudil, na Jam’iyyar APC, ya shigar gabanta, ya na ƙalubalantar nasarar sabon zaɓaɓɓen Ɗan Majalissar yankin, na Jam’iyyar NNPP, Abdulhakim Kamilu Ado.

Kotun ta kuma buƙaci masu ƙara da su biya tarar Naira Dubu Ɗari Takwas (800,000) ga Sabon ɗan majalissar, da ma hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ake ƙara, sakamakon ɓata musu lokaci da su ka yi.

Kotun dai, ta kori ƙarar ne bisa abinda ta kira da rashin gabatar da gamsassun hujjojin da za su tabbatar da ikirarin masu ƙara na rashin sahihancin hanyar tsayawa takara ga ɗan majalissar.

Kotun mai Alƙalai uku ƙarƙashin Jagorancin, Mai Shari’a Ngozi Flora, ta bayyana cewar, doka ta bawa kowacce Jam’iyya damar sauya ɗan takararta, idan aka samu dalili na mutuwar wani ɗan takara, ko da kuwa babu sunan sabon ɗan takarar a jerin sunayen da ke jikin takardun da Jam’iyya ta shigarwa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), muddin dai jam’iyyar ta samar da wannan ɗan takara ne ta hanyar da doka ta tanada.

“Saboda haka mun kori wannan ƙara, saboda rashin gamsassun hujjoji”, a cewar Mai Shari’a Ngozi, ya yin zartar da hukunci.

Har ya zuwa lokacin da mu ke rubuta wannan rahoto kuma, tsagin tsohon ɗan majalissar basu bayyana matsayarsu kan wannan hukunci da Kotun ta zartar, a yau (Alhamis), 7 ga watan Satumba ba.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button