Da Ɗumi-Ɗumi: Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Jaddada Nasarar Da Nasiru Gawuna Ya Samu, A Kotun Farko
Da safiyar yau (Juma’a) ne, kotun ɗaukaka ƙara, da ke babban birnin tarayya Abuja, ta sake jaddada nasarar da Ɗan takarar Gwamnan jihar Kano, ƙarƙashin jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna ya samu, a Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar.
Kotun ta kuma kori ƙarar da ɗan takarar jam’iyyar NNPP, a zaɓen Gwamnan jihar da ya gabata tun a watan Maris ɗin wannan shekarar, Abba Kabir Yusuf ya ɗaukaka, ya na ƙalubalantar nasarar da Kotun farko ta bawa Nasiru Gawuna.
Idan za a iya tunawa dai, a ranar 20 ga watan Satumbar wannan shekarar ne, Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar ta Kano, ta soke nasarar da, Abba Kabir Yusuf na NNPP ya samu, tare da ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen jihar, bayan da ta soke sama da ƙuri’u 165,000 daga cikin ƙuri’un da Abba Kabir Yusuf ɗin ya samu, bisa hujjar rashin sitamfi, da sanya hannun jami’an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).
Hakan kuma, ya sanya Abba Kabir Yusuf ɗin ta hannun Lauyansa, Wole Olanipekun, garzayawa gaban Kotun ɗaukaka ƙarar, ya na roƙonta da ta jingine hukuncin ƙaramar Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar.
A yau ne kuma, Kotun ɗaukaka ƙarar ta zartar da hukuncin da ya sake bawa, Nasiru Gawuna na APC ɗin nasara.