Labarai

Da Ɗumi-Ɗumi : Motar Da Ta Kwaso Ɗaliban Najeriya Daga Sudan, Ta Kama Da Wuta

Guda daga cikin motocin da su ka kwaso al’ummar Najeriya, da ke maƙale a Khartoum, babban birnin ƙasar Sudan, zuwa filin sauka da tashin jiragen sama, domin tsallakawa zuwa ƙasar Saudi Arabia, ta kama da wuta, da safiyar yau (Litinin).

Motoci guda Ashirin da Shida da ke ɗauke da al’ummar Najeriyar da su ka maƙale dai, sun bar Al Razi ne, da misalin ƙarfe 12:00 na daren ranar Litinin, zuwa Port Sudan.

”Guda daga cikin motocin da ke ɗauke da ɗaliban Najeriya 50, wacce ta taso daga Sudan, kuma ta nufi Port Sudan, da nufin kwaso al’ummar Najeriya rukuni na biyu, ta gamu da matsala, bayan da ta ɗauki zafi.

”Dr Hashim Idris Na’Allah, wanda ke kasancewa shugaban ƙungiyar Dattijan Najeriya a Sudan, ya kasance guda daga cikin fasinjojin motar, mai ɗauke da lambar Katsina, wacce kuma ke ɗauke da jimillar ɗalibai 50 (49 Maza, 1 Mace).

”Lamarin ya kuma faru ne, da misalin ƙarfe 2:30 na dare, Agogon Sudan.

”Direban ya kuma tsayar da motar, a kusa da shingen binciken RSF, kafin fashewar tayar motar, wacce ta haifar da kamawar wuta.

”Dukkannin fasinjojin sun fita daga motar lafiya.

”Daga bisani kuma an raba Arba’in daga cikin fasinjojin motar guda 50, ga wasu motocin na daban, da ke Aikin kwaso ɗalibai, ya yin da sauran Goman kuma, su ka kwana a wurin da lamarin ya faru, tare da Direbansu.

”Ɗaliban sun kuma ce Jami’an RSF, sun yi dukkannin mai yiwuwa wajen taimakonsu, har ma da basu kofunan shayi, da safe, kafin su bar wurin”, a cewar Sani Aliyu, wanda ke ƙasar ta Sudan.

Tuni kuma, Ɗaliban su ka bar wurin, tare da cigaba da tafiyar su zuwa tashar ta Sudan.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button