Da Ɗumi-Ɗumi : Zaɓaɓɓen Gwamnan Kano, Ya Shawarci Bankuna Su Daina Bawa Gwamnati Bashi
Zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci bankuna, da masu bada lamuni, da su gujewa bawa Gwamnatin jihar Kano mai barin gado bashi, batare da sanin Gwamnati mai jiran gado ba, tun daga ranar 18 ga watan Maris ɗin da ya gabata, har ya zuwa 29 ga watan Mayu, da za a miƙa mulki ga sabuwar Gwamnati.
Bayanin hakan kuma na ɗauke ne ta cikin wata sanarwa, da zaɓaɓɓen Gwamnan Kanon ya wallafa, a shafinsa na Facebook, da tsakiyar daren Asabar.
Inda saƙon ya ke cewa, ”Muna bawa bankuna da masu bada bashi ko lamuni na gida da ƙasashen ƙetare shawara akan su kauce wa bai wa Gwamnatin Kano mai barin gado bashi ba tare da sanin gwamnati mai jiran gado ba, daga 18 ga watan Maris zuwa 29 ga watan Mayu, 2023 – AKY”.
Wannan saƙo na zaɓaɓɓen Gwamnan kuma na zuwa ne, kwana guda, bayan da ya buƙaci masu gini a filayen makarantu, maƙabartu, da kasuwanni su ma su dakata.
Kuma tuni wancan umarni nasa ya samu martani daban-daban daga ɓangaren Gwamnati, inda har gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewar, ba a Gwamna biyu a jiha ɗaya, dan haka akwai buƙatar sabon Gwamnan mai jiran gado, ya jira har a rantsar da shi.