Kasuwanci

Da Ɗumi-Ɗumi : Za a Fara Sayar Da Tumatir A Kasuwar Muhammadu Buhari, A Farkon Watan Gobe

Akwai yiwuwar fara saukewa tare da sayar da Lemu, Tumatir da dango-ginsu a sabuwar kasuwar Muhammadu Buhari International Market, da ke ƙaramar hukumar Karu a Jihar Nasarawa, a farkon watan gobe, bayan an rantsar da sabuwar gwamnati.

Wata majiya mai ƙarfi ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta Nasarawa ta bada damar sauke kayan ne domin samun walwalar Al’ummar jihar, tare da samarwa matasa ayyukan yi, wanda hakan zai ragewa Matasan jihar zaman kashe wando.

Ana kyautata zaton kuma kasuwar zata iya samarwa da jahar kuɗin shiga da ya haura Naira Biliyan guda, a duk shekara muddin dai aka sakar mata mara.

Ko me ne ne fatanku?

Ku bayyana ra’ayoyinku a comment section.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button