Tsaro

Da Yawan Matasan Da Ke Neman Aikin Ƴan Sanda, Ba Sa Iya Rubuta Sunayensu – PSC

Hukumar ƴan sanda ta ƙasa (PSC), ta bayyana cewar, ta tantance aƙalla matasa 136,177 da ke neman gurbin Aikin Constables a rundunar ƴan sandan ƙasar nan, tun bayan fara gudanar da aikin tantance masu neman aikin da ta yi, a ranar 8 ga watan Janairun da mu ke ciki.

Kakakin hukumar na ƙasa, Ikechukwu Ani, shi ne ya bayyana hakan a ranar Talata, inda ya ce zuwa yanzu hukumar ta ɗora bayanan matasa 108,768 daga cikin wancan adadi da ta tantance.

Ya kuma ƙara da cewar, matsalolin sadarwa ne su ka hana hukumar ɗora bayanan sauran matasan da ta tantance ma.

Hukumar ta ƴan sanda, na aikin tantance matasa kimanin 416,270 ne dai, waɗanda su ka nuna sha’awar su ta yin aikin da rundunar ƴan sandan ƙasar nan.

“Yanzu ana yi wa matasan da ke neman wannan gurbin Aiki tantancewar Ido da Ido ne, kafin kuma zuwa ga matakin jarrabawa, da sauran matakai, ciki kuma har da gwajin lafiya.

“Ana kuma ɗora sakamakon dukkannin matasan da aka tantance kaitsaye a shafin hukumar ƴan sanda, wanda ke ƙarƙashin kulawar kwamitin sanya idon da shugaban hukumar, Solomon Arase ya kafa”, a cewar Ani.

Ani, ya kuma ce rundunar tana matuƙar mamakin yadda Ɗaliban da ke da kyakykyawan sakamakon kammala Sakandire na NECO da WAEC da dama, su ke ƙasa rubuta sunayensu, ko ma gabatar da kansu a taƙaice.

Ya kuma ce, jarrabawar da hukumar za ta shiryawa matasan ce za ta taimaka wajen tantance ƙwazon matasan da ya kamata rundunar ta ɗauka aiki.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button