Siyasa

Dalilai 3 Da Su Ka Bawa Abba Ƙwarin Gwuiwar Rusa Wasu Tsarukan Gwamnatin Ganduje

1. Sanin kowa ne tsohon gwamna Ganduje ya butulcewa Kwankwaso ne a karon farko bayan samun nasarar zama gwamnan Jahar Kano a 2015, yanzu Kwankwaso yayi nasaran kaudashi da goyon bayan Kanawa bayan ya maye gurbinsa da Abba K. Yusuf.

2. Sarakunan Jahar Kano… Sanin kowa ne babu wanda ya zabi Abba alhalin yana mai goyon sabbin sarakuna su dore, bayan yasan suma sabbin sarakunan sunyi iya bakin kokarinsu wajen ganin Abban baiyi nasarar zama gwamnan Kano ba, yayinda kowa yasan cewa tsohon Sarkin Kano Sunusi yana tare da Abba dari bisa dari kuma yayi iya yinsa da duk abinda zai iya domin ganin Abba yayi nasarar zama gwamnan Kano.

3. Wadanda suka sayi kadarorin gwamnatin Ganduje irinsu filayen makarantu, makabartu, kasuwanni, badala, Masallatai da sauransu. Duk wadanda suka san sun sayi wadannan kayayyakin musamman makarantu zakuga babu yaransu a wadannan makarantun.

La’akari da wadannan dalilan guda 3, zaku iya amincewa dani cewa tsohon gwamna ganduje yayi iya abinda zai iya domin ganin Abba bai yi ba inda yaso Gawuna ya gajeshi domin dorewar tsare tsarensa da suka hada da sabbin Sarakuna guda 5, sai da makarantu da makamantansu, Malamai da suma suka shiga tsamo tsamo domin kare muradin Ganduje da sauransu, amma inaaaa! hakan baisa sun samu nasara ba.

Saboda haka Abba a cigaba da abinda ya dace kawai.

✍️@Sani Ahmad Zangina @editor@ Karamchi @

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button