Damar Aiki: Jami’ar Bayero Na Neman Magatakarda
Jami’ar Bayero da ke birnin Kano, ta fitar da sanarwar neman wanda zai riƙe muƙamin Magatakarda (Registrar), daga ciki, da wajen Jami’ar.
Wannan buƙata dai, na ɗauke ne ta cikin wata sanarwa da Jami’ar ta fitar, a ranar Laraba, 13 ga watan Satumban 2023, da ke ɗauke da sa hannun Shugabanta, Farfesa Sagir Adamu Abbas.
Sanarwar dai, ta bayyana cewar, Wajibine ga dukkannin wanda ke sha’awar rabauta da wannan muƙami, ya kasance ya na da sakamako mai kyau a takardarsa ta kammala karatun Digiri, Sannan dole ne ya kasance ya yi karatun gaba da Digiri (Postgraduate).
Ƙarin abubuwan da ake buƙata su ne; ya kasance ya na da ƙwarewar Aikin gudanarwa aƙalla na tsawon shekaru 15 a Jami’a, Kuma ya kasance ya kai matakin Mataimakin Magatakarda (Deputy Registrar) ko sama da haka.
Bugu da ƙari, wajibi ne ya kai aƙalla shekaru 60 da haihuwa, tare da kasancewa ƙwararre ta fuskar amfani da fasahar tattarawa da Adana bayanai ta zamani.
Dukkannin wanda ya samu rabauta da wannan muƙami dai, zai yi aiki ne a matsayin shugaban sashen tattara bayanai da adana su na Jami’ar, Kuma za a dinga biyansa Albashi dai-dai da yadda tsarin Albashin Magatakarda ya ke, a Jami’o’in tarayyar Najeriya.
Ka zalika, zai shafe tsawon shekaru 5, a wannan muƙami.
Waɗanda ke da sha’awar nema, za su kai kwafi 20 na takardar nuna sha’awa (Application Letter), da bayanan Ayyukan da aka gudanar (Personality Profile), da ma takardun Makaranta, a cikin Envelope, a kuma rubuta “POST OF REGISTRAR”, a ɓangaren dama, daga sama, a kuma sanya Adireshin:
The Vice Chancellor
Bayero University
PMB 3011, Gwarzo Road
Kano – Nigeria.
Sannan akwai buƙatar waɗanda ke neman wannan muƙami, su sanya Uku daga cikin Referees ɗinsu, su aike da rahoton shaida akansu, zuwa Ofishin Shugaban Jami’ar.
KU SANI: Za a rufe karɓar takardun nuna sha’awa cikin makonni 6, bayan fitar da wannan sanarwa.