DAMAR SAMUN HORO A FANNIN NOMA DA KIWO, TARE DA ALAWUS A KOWANNE WATA
Makarantun horas da Matasa kan sana’o’in dogaro da kai, ta fuskar noma da kiwo, da ke jihohin Kano, Gombe, Osun, da ma babban birnin tarayya Abuja, ƙarƙashin gidauniyar LEVENTIS FOUNDATION, wacce aka samar tun shekarar 1987, sun buɗe damar neman gurbin karatun Certificate na tsawon shekara guda (Wata Tara), a fannoni daban-daban da ke da alaƙa da noma da kiwo.
Ana kuma neman gurbin karatun ne a kyauta, haka zalika, za a bayar da horon shi ma kyauta, baya ga tagomashin kuɗaɗen alawus na Naira 10,000 kowanne wata, ga ɗaliban da su ka samu nasarar shiga guda daga cikin waɗannan makarantu.
Haka zalika, wurin kwana, da abinci kyauta ne, a tsawon lokacin ɗaukar horon, kuma akwai ƙaramin jari na Naira 30,000 da ake bawa Ɗaliban da su ka samu nasarar kaiwa ƙarshen zangon ɗaukar horon.
ABUBUWAN DA AKE BUƘATA DOMIN SAMUN GURBI
•Wajibi ne dukkannin wanda zai nemi guda daga cikin waɗannan makarantu ya kasance lafiyayye, a zahiri, da ƙwaƙwalwarsa.
•Wajibi ne ya kasance ya na iya karatu da rubutu, musamman ma na Turanci (muna ganin kamar wanda ya kammala makarantar Sakandire zai cika wannan sharaɗi).
•Wajibi ne shekarunsa su kasance daga 18 zuwa 40.
•Wajibi ne ya samu nasara, a jarrabawar rubutu, da ta baki da baki (Oral) da za a gudanar, kafin ɗaukar ɗalibai.
•Wajibi ne ya kasance mai sha’awar fannin noma da kiwo.
•Shaidar ƙwarewa, ko wani abu da ya ke da alaƙa da noma tun daga tushe, ya na da muhimmanci (ba dole bane).
YADDA AKE NEMAN MAKARANTUN
Dukkan wanda ya cika waɗancan sharuɗɗan da mu ka lissafa a sama, zai rubuta wasiƙar nuna sha’awa, ɗauke da sa hannun shugaban ƙaramar hukumar da ya fito, ko Sakatarenta, tare da hotunansa guda 2, da kwafin takardun makaranta ko wasu takardu da ya mallaka guda uku, sannan ya kai takardar guda daga cikin adireshin makarantun da za mu lissafo a ƙasa (wacce ya ke sha’awa) :
• LEVENTIS FOUNDATION KANO STATE AGRICULTURAL TRAINING SCHOOL, DA KE GARIN PANDA, A ƘARAMAR HUKUMAR ALBASU, P.M.B. 3555, KANO, A JIHAR KANO.
• LEVENTIS FOUNDATION GOMBE STATE AGRICULTURAL TRAINING SCHOOL TUMU, ƘARAMAR HUKUMAR AKKO, A JIHAR GOMBE.
• LEVENTIS FOUNDATION OSUN STATE AGRICULTURAL TRAINING SCHOOL IMO, P.M.B. 5074, ILESA JIHAR OSUN.
• LEVENTIS FOUNDATION FCT AGRICULTURAL TRAINING SCHOOL YABA, ABAJI AREA COUNCIL, P.M.B. 001, ABAJI, ABUJA.
• THE GENERAL MANAGER (TECHNICAL AND TRAINING) LEVENTIS FOUNDATION (NIGERIA) LTD/GTE NO 2, LEVENTIS CLOSE, CENTRAL BUSINESS DISTRICT, P.O.Box 20351, GARKI ABUJA, FCT.
www.leventisfoundation.org.ng
Ƙari akan horon na shekara guda kuma, Makarantun na Leventis Foundation (Nigeria), su na bada ƙananan horo a fannoni daban-daban na noma da kiwo, kamar: Sarrafa Amfanin Gona Da Adana shi (Processing & Packaging); Kiwon Kaji (Poultry Production), Noman Kayan Lambu (Vegetables Production), Kiwon Ƙudan Zuma (Bee-Keeping), Samar Da Zuma (Honey Production), Kiwon Kifi (Fish Farming), Mushrooms Production, Value Chain Development, Yadda Ake Haɗa Abincin Dabbobi (Food Formulation), Noma A Gonar Tafi Da Gidanka (Greenhouse Farming and Hydroponics), Urban Farming and Climate-Smart Agriculture, da makamantansu.
Za a rufe rijista a ranar: Juma’a, 15 ga watan Disamban 2023.
Za a gudanar da jarrabawa da tantancewa, a ranar Asabar 16 ga watan Disamba.
KU SANI : DUKKA MAZA DA MATA, SU NA DA DAMAR CIKEWA.
✍️ MIFTAHU AHMAD PANDA
08039411956.