Damfara: Kotu Ta Ɗaure Ɗan Yahoo Tsawon Shekara Guda
Ukoh Michael Odeh, da ke gudanar da ayyukan zamba a kafafen intanet (Yahoo), ya samu tikitin zama a gidan gyaran hali, har na tsawon shekara guda, bayan da hukumar yaƙi masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) reshen Makurɗi ta gurfanar da shi a gaban Kuliya.
Odeh, ya gurfana ne, a gaban Mai Shari’a O.A. Egwuatu, na babbar Kotun tarayya, da ke Maitama, a Abuja.
An kuma daƙume shi ne, bayan da hukumar ta EFCC ta samu rahoton ire-iren ayyukan zambar da ya ke gudanarwa, a kafafen sadarwa na Intanet, a garin na Makurɗi.
Cajin da aka karanta masa a gaban kotun dai na cewa, “Kai Ukoh Michael Odeh, tsakanin shekarar 2022 zuwa 2023 a Makurɗi, da ke Jihar Benue, an gurfanar da kai a gaban wannan Kotu Mai Adalci ne, bayan da ka gaza bayyana inda ka samo kimanin Naira Miliyan 6, da aka samu a Asusun Bankinka na FCMB, Mai lambar: 4668442010, ya yin da ake zarginka da mallakar kuɗaɗe ta haramtattun hanyoyi, musamman ma na zamba, a kafafen Intanet. Wanda ya saɓa da sashe na 20 (a) na tanade-tanaden dokar mallakar kuɗaɗe ta shekarar 2022, inda sashe na 20 (b) na dokar ya yi tanadin hukuncin aikata wannan laifi”.
Bayan karanta masa laifin da ake zarginsa da shi ne kuma, sai wanda ake zargin ya amsa. Inda Lauyan masu ƙara mai suna, M. Yusuf, ya roƙi kotun da ta zartar masa da hukunci, tunda ya amsa laifinsa.
Anan ne kuma, Alƙali Egwuatu, ya yanke wa Odeh ɗin hukuncin zaman gidan waƙafi na shekara guda, ko tarar Naira 300,000.
Ka zalika, Kotun ta buƙaci mutumin da ya miƙa wata waya ƙirar Infinix Smart 7 ga Gwamnatin tarayya, bayan da aka tabbatar da cewar, ita ma an same ta ne, ta waccar hanya.