Ƙasashen Ƙetare
Davido Ya Samu Izinin Zama Ɗan Ƙasar Amurka
Fitaccen Mawaƙin nahiyar Afirka, ɗan asalin Najeriya, David Adeleke, da aka fi sani da Davido, ya samu halartar zaman Majalissar jihar Georgia, ta ƙasar Amurka inda aka bayyana shi a matsayin ɗan ƙasar.
Mawaƙin shi ne ya bayyana haka, ta shafinsa na Instagram, a ranar Juma’a.
Inda ya wallafa cewar, “Da safiyar nan, na sai halartar zaman gamayyar Majalissun tarayya, da na Dattijai, a jihar Georgia, inda aka bayyana ni a matsayin ‘ɗan ƙasa’… Ubangiji shi ne abin godiya”.
Hakan dai, wata dama ce da al’ummar ƙasashe da dama ke amfana, ta zama fiye da ƴan ƙasa ɗaya (Dual Citizenship).