Ƙasashen Ƙetare

Dogari Ya Harbe Minista, A Uganda

Guda daga cikin Dogaran ƙaramin ministan Ayyuka, da Masana’antu na ƙasar Uganda, Kanal Charles Okello Engola, ya harbe shi har Lahira, a ranar Talata.

Kakakin rundunar ƴan sandan ƙasar ta Uganda, Fred Enanga, ya ce lamarin ya faru ne a ya yin da Ministan ya ke yunƙurin shiga motarsa domin tafiya wurin aiki.

Jami’in hulɗa da jama’ar ya kuma ce, tuni aka ƙaddamar da bincike kan lamarin, ya na mai ƙarawa da cewar, tuni ƙwararru a fagen binciken ayyukan ta’addanci su ka ziyarci wurin da mummunan al’amarin ya auku, kuma ana sa ran za su yi amfani da fasaha wajen gano ainihin dalilin kisan.

Wani shaidar gani da ido dai, ya ce Sojan ya yi ƙorafi ne kan gaza biyansa haƙƙoƙinsa na albashi, kafin kuma Ministan ya ci zarafinsa, wanda ya jawo ya yi amfani da bindiga wajen harbe shi.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button