Doka Ta Taka Doka: Ana Zargin Mabiyan Ɗan Majalissa Da Lakaɗa wa Jami’an Kotu Duka
Wasu ɓata gari, da ake kyautata tsammin yaran Ɗan Majalissar Dokoki mai wakiltar Keffi ta yamma, a jihar Nasarawa, Honourable Baba Ali Nana ne, sun lakaɗa wa Masinjan kotu, mai suna Malam Dauda duka, tare da wani mutum guda, ya yin da su ka halarci kasuwar Ƴan Lemu, da ke garin Mararaba, a ƙaramar hukumar Karu, ta jihar Nasarawa, domin liƙa takardar sammaci, kamar yadda kotu ta umarce su.
Tun da farko dai, a wata kara mai lamba NSD/MG.177/2023 wadda wani ɗan kasuwa mai suna, Alhaji Sani Zangina ne, ya shigar a gaban Babbar Kotu mai lamba 3, da ke Mararaba, yana ƙalubalantar ɗaukacin Shuwagabannin kasuwar, ciki kuwa har da shi wancan ɗan majalissa (Honourable Baba Ali Nana), da ma dukkannin ƙungiyoyin da ke da rijista gami da lasisin gudanar da hada-hadarsu a kasuwar, dama mallakar filin ba bisa ka’ida ba.
Sai dai, a ya yin da Jami’an Kotun su ka halarci kasuwar domin manna takardar sammaci, a jikin ƙofar shiga, kamar yadda kotu ta umarta, sai wasu ɓata gari (da ake kyautata zaton yaran wancan ɗan majalissa ne), su ka far musu, tare da tsitstsinka musu mari (har sai da su ka ga wuta), gami da karɓe makullin babur din da suka halarci kasuwar da shi, domin aiwatar da wannan aiki.
Jami’an kuma, ba su samu sukunin barin wannan kasuwa ba, har sai da wani Dattijo a kasuwar ya sanya baki, a cikin lamarin, kafin ɓata garin suka barsu suka fice, ba tare da aiwatar da umarnin da kotun ta aiko su, na liƙa takardar sammaci ba.
Kafin aukuwar hakan dai, dama sai da Sarkin Hausawan Mararaba, Alhaji Usman Mani, ya yi gargaɗi ga Jami’in Kotun, a ya yin wata tattaunawa da su ka yi, da Shugaban Sashen Tsaron Kasuwar, Abdullahi Mai Gada, Inda a minti na 1 da daƙiƙa 28 na tattaunawar tasu, bayan miƙa wayar salula ga Ma’aikacin Kotun, Alhaji Mani ke gargaɗin Ma’aikacin da kada ya kuskura ya halarci kasuwar domin liƙa wannan sammaci, har ya na cewa ”Dauda ka riƙa taka tsan-tsan a wannan Aiki, ina gaya maka, Na rantse maka da Allah, ka da mu sa a cire ka daga Kotun nan a kaika wani Ƙauye, Ka da in gaya wa Jimo, zan gaya wa Jimo maganar nan…”, wanda hakan abu ne da ya ke bayyana barazana ga ma’aikacin ƙarara.
Ba ya ga haka, a mintuna na 10 da daƙiƙa 36 na tattaunawar tasu, Alhaji Mani, ya kuma bayyana cewar, daga cikin mutanen da ke kasuwar tasu ta Ƴan Lemu, ”Akwai Ƴan giya, Akwai Ɗan ƙwaya, akwai wanene, akwai wanene, wani bamu san da me ya zo wurin ba, a zo ace an zo an kashe wani, ko an zo an yi wata maganar banza, ko a zo a ɗauki wani mataki wanda za a raunata wani, ya yi kyau ?”.
Sai dai ko da Babban Editan Jaridar Rariya Online, Miftahu Ahmad Panda, ya tuntuɓi Sarkin na Hausawan Mararaba, Alhaji Usman Mani, domin jin ta bakinsa game da waɗannan kalamai da ake zargin ya furta, sai ya ɓuge da faɗa, gami da barazanar maka wannan gidan Jarida a gaban Kuliya.
Ka zalika, shi ma Honouble Baba Ali, wanda ake zargin yunƙurin isar da takardar sammaci gare shi ne ya haifar da wannan sa toka sa katsi, ya gaza ɗaukar wayar da Jaridar Rariya Online ta yi ta maka kwaɗa masa, inda ya buƙaci da a aike masa da gajeren saƙon SMS, sai dai duk da aike wannan gajeren saƙo da mu ka yi, har ya zuwa lokacin da mu ka wallafa wannan rahoto, bamu samu wata amsa daga Ɗan Majalissar, wanda kuma ke zama shugaban kasuwar kan matakan da su ka ɗauka, ko za su ɗauka domin kiyaye aukuwar irin hakan a nan gaba ba.
Bugu da ƙari, shi ma Shugaban sashen kula da tsaro na Kasuwar, Abdullahi Mai Gada, katse wayar wakilinmu, Miftahu Ahmad Panda ya yi, jim kaɗan bayan bayyana masa buƙatarmu ta jin ta bakinsa.
Tuni dai, Sakataren Kwamitin Shari’a, Yahaya Yakubu Shafa Esq., ya tabbatar da aukuwar wannan lamari marar daɗin ji, ya na mai alƙawarta yin dukkannin mai yiwuwa, wajen ganin an ɗauki matakan da su ka dace game da lamarin.
©️Rariya Online 22-Mayu-2023