Zamantakewa

Dokar Rage Kashe Kuɗaɗe A Ya Yin Aure, Za Ta Magance Matsalar Yawaitar Cikin Shege – Ɗan Majalissar Sokoto

Abubakar Shehu, wanda ke wakiltar yankin Yabo, a majalissar dokokin jihar Katsina, wanda kuma ke zama shugaban kwamitin majalissar kan al’amuran Addinai, ya bayyana irin alfanun da ya ke sa ran za a samu, idan aka amince da ƙudurin dokar rage kuɗaɗen da ake kashewa, a ya yin Aure.

Inda ya ce, ɗan uwansa, da ke wakiltar yankin Gudu, Faruk Mustapha Bale ne ya gabatar da ƙudurin dokar, wacce ke buƙatar a yi gyara kan dokar Aure, wacce aka samar a shekarar 1992, tare da yi mata kwaskwarima a 1996.

Ya kuma ce, sun ga dacewar goyon bayan amincewa wannan ƙudurin doka ne, sakamakon irin yanayin da al’ummarmu ke tsintar kansu, wajen shiga matsi a ƙoƙarin yin bajintar ke ce raini, ya yin Aure.

Ka zalika, ɗan majalissar ya ce, bayan miƙa bayanin ƙudurin ga Fadar Mai Alfarma Sarki Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar Na III, Sarkin ya yi maraba da wannan ƙudiri nasu, tare da umartar Shugaban Kwamitin Harkokin Addinai na Fadar sa, Farfesa Sambo Junaid, ya basu dukkannin wani goyon baya, ko gudunmawar da su ke buƙata.

”Kuma muhimmancin ƙudurin dokar ne, ya sa tuni majalissar dokokin ta yi masa karatun farko, da na biyu, bayan miƙa shi ga kwamitin al’amuran Addinai na Majalissar, wanda na ke jagoranta. Mun gayyaci masu ruwa da tsaki daban-daban, da su ka haɗarda Malamai, Masana, ɗariƙu, da ma ƙungiyoyi, mu ka bayyana musu ƙudurinmu, kuma su ka karɓa, tare da yin farinciki da shi.

”Bayan tattaunawarmu da masu ruwa da tsakin kuma mun zauna, mun rubuta rahotonmu game da ƙudurin, tare da gabatar da shi a gaban majalissa, inda hakan ya bada damar sahalewa ƙudirin, ya koma doka, wanda a yanzu sanya hannun Gwamna (Aminu Tambuwal) kawai ta ke jira”, a cewar Shehu Yabo.

Ko da aka tambaye shi, irin alfanun da ake sa ran dokar za ta kawo, ɗan majalissar ya ce dokar za ta bada manyan gudunmawoyi, ”misali a yanzu, idan ka ga yarinya kana so, domin Iyayenta fa su san Auren ƴar su za ka yi, to dole sai ka kashe maƙudan kuɗaɗe. Wasu lokutanma za ka iya ganin Motoci uku zuwa huɗu maƙare da kayayyakin sha daban-daban, Goro, da sauran abubuwa. Wanda a zancen gaskiya hakan ya na damun samari, kuma su na ƙorafi akai”.

Inda ya ce, idan dokar ta samu sahalewa, to Ango abu biyu kawai zai dinga bayarwa a ya yin ɗaurin Aure, wato Goro da katan ɗin Lemuka guda biyu. Dukkannin sauran tsarabe-tsarabe, da kashe kuɗi a ya yin Aure, Bikin Suna, Bikin Kaciya, da ma sauran bukukuwa za a haramtasu.

Ka zalika dokar za ta haramta yin dandazon Maza da Mata a ya yin gudanar da irin waɗancan bukukuwa.

Ya kuma ce, dokar bata saɓawa Addini ko Al’ada ba, hasalima za ta kare yawan mace-macen Aure, da cikin da ƴan mata kan yi, ba tare da Aure ba, sakamakon rashin kuɗin Aure daga samarinsu.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button