DSS Sun Bankaɗo Maɓoyar Ƴan Ta’adda, A Kano
Rundunar tsaron farinkaya DSS, hadin gwuiwa da hukumar Sojin kasa, da ta Yan Sanda, sun bankado maboyar yan taádda a jihohin Kano, da Kaduna.
Gamayyar rundunonin sun gudanar da wannan gagarumin Aiki ne dai, da safiyar ranar Litinin. A ya yin da jamián su ka kai sumame maboyar a Kaduna dai, guda daga cikin yan taáddan da ke dauke da karamar riga ya mayar da martani, wanda ya haifar da sake rincabewar lamarin.
An kuma samu nasarar dakume uku daga cikin yan taáddan da ake zargi, a ya yin sumamen.
A ya yin da Jamián su ke gudanar da bincike bayan kammala fatattakar yan taáddan dai, an samu bindigu kirar AK-47 guda biyu, da kuma karama kirar PISTOL, tare da karamar Naúrar kwamfiyuta kirar cinya wato LAPTOP.
Bayanin hakan kuma, na dauke ne ta cikin wani jawabi da Kakakin rundunar DSS, Peter Afunanya ya sanyawa hannu.